Isa ga babban shafi
Libya

Sabbin Shugabannin Libya sun yi alkawarin mayar da doka da oda

Shugaban Kasar Libya, Muammar Gaddafi, wanda aka kawar daga madafun iko, ya yi kira ga magoya bayan sa, da su kaddamar da yakin sunkuru kan 'yan tawayen da suka kwace ragamar tafi da kasar.A jawabin da ya yiwa 'yan kasar ta radiyo, dan bikin cika shekaru 42 da karbar ragamar tafi da kasar, Gaddafi ya shaidawa 'yan tawayen da su saurari harin sari ka noke, wanda zai basu nasara kan su.A bangare daya kuma Ministan harkokin wajen Gaddafi, Abdelati Obedi, ya ajiye aikin sa.Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya sanar da sakewa 'Yan Tawayen Libya kudin kasar da suka kai Dala biliyan 15.Yayin da yake jawabi wajen taron kasahsen duniya da aka yi kan kasar ta Libya, shugaban ya bayyana cewar, mun mika kudaden mutanen Libya da aka sace ga 'yan kasar Libya.An kammala taron kasashen duniya sama da 60 a Paris na kasar Faransa, da niyyar tallafawa kasar ta Libya, domin farfadowa bayan yaki da aka yi domin kawar da Shugaba Muammar Gaddafi.Shugaba Nicolas Sarkozy ya nemi Shugabannin ‘yan tawayen kasar dasu maida hankulansu wajen dinke duk wata baraka da hada kan jama'a.A cewar Nicolas Sarkozy Shugabannin kasashen da wakilan wasu su sama da 60 sun amince a maidawa Libya dukkan kudaden da suka adana a kasashen su saboda a sake gina kasar.A nasa jawabin bayan taron PM kasar Birtaniya David Cameron cewa ya yi dakarun kawance na kungiyar OTAN/NATO zasu ci gaba da zama a Libya, don kare fararen hula.Shima dai Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon cewa ya yi akwai bukatar daukan matakan da suka wajaba domin kare fararen hulan Libya.Rusha da China wadanda suka soki NATO saboda kutse cikin Libya yanzu dai sun bi sahu domin har Rusha tac e zata yi kawance da Majalisar Rikon kwaryar Libyan.Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, ta ce ba zata amince da 'Yan Tawayen Libya a matsayin halartattun shugabanin kasar ba.Shugaban gudanarwar kungiyar, Jean Ping ya bayyana haka, a taron da aka yi a Paris, inda yake cewa, sun zuba ido suga yadda 'Yan Tawayen zasu yi da bakaken fatar dake aiki a Libya. 

Shugaban Rikon Kwaryar Libya Mustapha Abdeljalil da Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban Rikon Kwaryar Libya Mustapha Abdeljalil da Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy MIGUEL MEDINA / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.