Isa ga babban shafi
Libya

Tsohon Ministan harkokin Wajen kasar Libya Shalgam ya ce Libya ce ta kai hari kan jirgin saman kasar Faransa

Tsohon Ministan harkokin Wajen kasar Libya, Abdel Rahman Shalgam, ya ce Libya ce ta kai hari kan jirgin saman fasinjan kasar Faransa cikin shekarar 1989, wanda ya hallaka fasinjoji 170.A wata hira da ya yi da Jaridar Al Hayata wanda aka buga yau Litinin, Tsohon Ministan ya ce dakarun Libya ne suka harbo jirgin, a kokarin da suke na kashe shugaban 'yan adawa, Mohammed Mohammed al Megrief.Shalgam ya kara da cewa, tunaninsu shine shugaban 'yan adawan na jirgin, amma daga bisani sai aka tarar ba ya ciki.Jirgin dai an harbo shine lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Brazaville na kasar Congo, daga birnin Paris na Faransa, ta Ndjamena babban birnin kasar Cadi, amma ya fadi a sararin samaniyar kasar Janhuriyar Niger, bayan wasu bama bamai sun tashi a ciki.Wata kotu a kasar Faransa ta daure wasu 'yan kasar ta Libya shida, rai da rai kan hadarin, yayin da Gwamnatin Libya ta amince ta biya diyyara Dala miliyan 170 ga iyalan wadanda ke cikin jirgin.Ministan ya ce, Libya ta na da hannu wajen harbo jirgin Lockerbie, tare da wasu kasashe.Tuni dai Shalgam ya kauracewa Shugaba Mummar Gaddafi, inda ya koma bangaren 'yan Tawaye. 

Latifa Mouaoued/RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.