Isa ga babban shafi
Libya

Mahukuntan Libya sun musanta cewa Shugaba Gaddafi zai ajiye mulki

Kasar libiya ta musanta labarin da jaridar kasar Rasha ta buga a jiya talata na cewa shugaban kasar Libiya Mammar Gaddafi na yunkurin mika mulki.Watanni biyar ke nan ana fafatawa tsakanin shugaban da yan tawayen kasar amma ko gezau, sai dai rahotanni bogin da ke nuna shugabna zai ajiye mulkisa na shekaru 41 bisa yarjejeniyar inhar za’a tabbatar masa da tsaro a ciki da wajen kasar.Sai sadi tuni mai magana da yawun gwamnatin kasar Libiya, Moussa Ibrahim ya karyata wannan labari da tushen ta tafi karfi daga kasar Rasha da Italiya.Inda yake cewa, Gadafi tarihi ne a kasar Libiya babu batun yarjejeniya a tsakaninmu da shi, kuma a shirye Libiya take da ta sadaukar da ranta da kare shi.Har’ila yau kuma rahotanni daga Asibitin al-Hakim dake Misrata ya nuna cewan duk da tattaunawan dake tsakanin gwamnatin kasar Libiya da yan tawayen, gawarwakin 'yan tawayen 11 ne aka kawo asibiti da kuma wasu 42 da suka ji raunika a jiya. 

Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi
Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi REUTERS/FIDE Press service
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.