Isa ga babban shafi
Libya

Kotun Kasa-Da-Kasa Ta Bukaci A Kama Gaddafi Na Libya

Kotun kasa-da-kasa dake Hukunta masu aikata laifukan yaki dake da cibiyarta a Hague ta yanke hukuncin a kama mata Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi.Kotun na tuhumarsa da laifukan cin zarafin jama’a da bada umarnin kaiwa fararen hula hare-hare a cikin watan biyu na wannan shekaran.Kotun ta kuma bada umarnin a kama mata wasu na hannun daman Shugaba Gaddafi su biyu da suka hada da dan sa  al-Islam da kuma jami’in leken asiri na kasar Abdullah al-Sanussi.Dubban mutane ne suka rasa rayukan su a rikicin kasar Libya.Shugaban Kotun Sanji Monageng yace akwai kwararan hujjoji dake nuna Shugaba Gaddafi da dan sa sun aikata ayyukan hashsha.Mai shigar da kara na kotun, Luis Moreno-Ocampo ya shigar da wannan karar cikin watan biyar data gabata. 

Shugaba Moammar Gaddafi na Libya
Shugaba Moammar Gaddafi na Libya RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.