Isa ga babban shafi
Libya

Kotun Kasa-da-Kasa Na Shirin Gurfanar da Masu Kisa A Kasar Libya

Yan tawayen dake yakan shugaban kasar Libya Mummar Gaddafi sun zargi dakarun kasar da hallaka mutane biyar cikin harin a garin Misrata.Wannan daidai da lokacin da babban mai gabatar da kara na kotun duniya, Luis Mareno-Ocampo ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa za'a nemi cafke wadanda ake zargi da lafin yaki daga bangarorin biyu.Majiyoyi sun bayyana yadda ake hallaka ‘yan kasashe Afrika, bada laifi ba, sai domin ana zarginsu da zama sojan haya na gwamnati.Akwai rohoto yadda wasu suka ci zarafin ‘yan Afrika a garin Benghazi da wasu birane tare da hallaka su.Akwai zargin mahukunta na Benghazi sun cafke ‘yan Afrika masu yawa, babu tabbaci ko mayaka ne ko kuma ‘yan ci rani. 

Mai gabatar da kara na kotun kasa-da-kasa  Luis Moreno-Ocampo
Mai gabatar da kara na kotun kasa-da-kasa Luis Moreno-Ocampo rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.