Isa ga babban shafi
Tunisiya

Bama Son Gyauron Gwamnatin Ben Ali-Inji Masu Bore

Masu boren gamagari a kasar Tunisia sun bukaci Fira Ministan kasar da yawa Allah ya kama gabansa kamar yadda Tsohon Shugaban kasar Ben Ali  ya tsere daga kasar zuwa kasar Saudiyya.Daruruwan masu boren, da karfin tsiya suka kutsa ofishin Fira Ministan Mohammed Ganochi inda sukayi ta lika bayanai dake cewa basa son muamulla da gyauron Ben Ali.Duk da lallashin da yayi tayi, masu boren  nata matsa lamba, cewa allambaran sai  ya ajiye aiki saboda irin rawar daya taka a zamanin hambararren Shugaba Ben Ali.A halinda ake ciki wasu bayanai na cewa wasu dangi da iyalan  tsohon Shugaba Ben Ali sun isa kasar Canada tun ranar Jumaa.Bayanan na cewa ciki akwai matar tsohon Shugaban da 'ya'yan su .     

Masu bore a Tunis na kasar Tunisiya
Masu bore a Tunis na kasar Tunisiya rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.