Fira Minista Yayi Alkawarin Sauka Bayan Zabe
Fira Ministan kasar Tunisia Mohammed Ghannouchi yayi alkawarin sauka daga mukamin ya daina siyasa kwata-kwata bayan an gudanar da zabe karkashin tafarkin democradiyya na farko tun samun ‘yancin kasar daga kasar Faransa a shekara ta 1956.Fira Ministan ya fada cikin wani shirin musamman na gidan Talabijin na kasar cewa yayi alkawarin ganin ya jagoranci yin zabe na farko a kasar.Ya fadi cewa za'ayi zabukan wakilan majalisa dana Shugaban kasa cikin watanni shida masu zuwa.Fira Ministan wanda yake rike da wannan mukami tun lokacin da hambararren Shugaba Ben Ali ya tsere makon jiya zuwa kasar Saudiyya, na wannan alkawari ne sakamakon kara boren gamagari, inda mutane ke neman dukkan wadanda sukayi zamani da tsohon Shugaban suyi bankwana da mulki.
Wallafawa ranar: