Isa ga babban shafi
Girka-EU

Yau Kasar Girka Zata Fara Karbar Tallafin Kudade

YAU ne ake saran kasar Girka, zata karbi kashin farko na kudaden tallafin da Kungiyar kasashen Turai da Hukumar Bada lamini ta duniya sukayi mata alkawari.Kwamishinan kula da kudade, Olli Rehn, yace yau zasu mikawa kasar Euro biliyan 20, kamar yadda aka amince da shi.A wani labari kuma, Gwamnatin kasar Girka ta kori mataimakin ministan kula da yawon bude ido, Angela Gerekou, saboda kaucewa biyan haraji.Rahotanni sun baiyana cewar, matar ministan ta kaucewa biyan harajin kudade sama da Euro miliyan biyar. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.