Isa ga babban shafi
Girka

Ana Cigaba Da Bore A Athens

Masu bore a Girka na cigaba da gudanar da zanga zangan gama gari a birnin Athens, inda suke kalubalantar matakan tsuke bakin aljihu da Gwamnatin kasar ta dorawa jama’a, duk da cewa ta karbo rancen kudin Turai daya kai Euro billiyan 110.Ministan Kodago na kasar  ya fadi cewa Gwamnatin kasar ta bullo da jerin matakan farfado da tattalin arzikin kasar ne domin ceton kasar daga durkushewa.Daga cikin matakan tsuke bakin aljihun akwai zabtare kudin da yakai Euro biliyan 30 daga kasafin kudaden kasar na tsawon shekaru uku daga bangaren maaikata da kuma wadanda sukayi ritaya.Gwamnatin ta kuma tsara karin kudaden haraji.A jiya Majalisar kasar Faransa, ta amince da shirin doka domin tallafawa kasar ta Girka da rancen da yakai Euro biliyan 16.8.Jamiyyar dake mulki UMP da kuma jamiyyar PS, awani mataki, da ba safai sukan dauka ba, sun hada kai domin baiwa kasar ta Girka wannan rance.Domin nuna goyon baya ga masu boren na Girka, daruruwan maaikata sun shiga yajin aiki na kwanaki biyu. Asibitoci da wasu maaikatu na wasu muhimman  ayyukan  ne kawai.A gobe ake kyautata zaton zanga zangan zaiyi kamari, saboda maaikata zasu bazama tituna domin nuna rashin jin dadinsu ga Hukumomi.  

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.