Isa ga babban shafi
Thailand

Mutun Daya ya Hallaka Yau Jumma’a Sakamakon wata Fashewa

Ma’aikatan aikin gaggawan da na lafiyar kasar Thailand sun bayyana cewa mutun daya ya hallaka, sakamakon tashin wani gurneti cikin yankin hada hadar kasuwanci na Bangkok babban birnin kasar da safiyar yau Jumma’a.Mataimakin PM kasar ya ce kawo yanzu mutane uku su ka hallaka daga jiya Alhamis, bayan samun fashewa biyar da su ka jijjiga masu zanga zangar da ke sanya da jajayen kaya, su na neman kirar sabon zabe.Akwai akalla mutane 75 da su ka jikata sanadiyar lamarin, Yan sanda da a ka tura domin shawo kan masu zanga zangar sun ja da baya, tuni kasashen Amurka, Birtaniya da Australia su ka gargadi Yan kasashen masu neman kai ziyara kasar Thailand saboda zamna zullumin da ake ciki. 

La police anti-émeutes thaïe se dresse face aux milliers de chemises rouges, protestataires anti-gouvernmentaux qui ont dréssé des barricades.
La police anti-émeutes thaïe se dresse face aux milliers de chemises rouges, protestataires anti-gouvernmentaux qui ont dréssé des barricades. Photo: Manpreet Romana/ AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.