Isa ga babban shafi

Dubban 'yan kasar Hungray na zanga-zangar bukatar a hukunta Katalin Novak

Al’ummar kasar Hungary sun fantsama kan tituna don gudanar da zanga-zanga da nufin tilastawa gwamnati mayar da shugaban wani gidan kula da kananan yara da ya yi wa yara da dama fyade zuwa gida yari.

Har yanzu dai gwamnati bata ce komai kan wannan lamari ba
Har yanzu dai gwamnati bata ce komai kan wannan lamari ba © Bernadett Szabo / Reuters
Talla

Tun farko shugabar kasar Katalin Novak ce ta yiwa mutumin da karin wasu mutane da ake kama su da laifin tare afuwa, dalilin da ya tayar da rikici a kasar.

Matsin lamba da shan chachaka ya tilastawa uwargida Novak da ministar shari’ar kasar sauka daga mukamin su, amma duk da haka jama’a na bukatar gwamnati ta mayar da mutanen da aka yiwa afuwar zuwa gidan yari, sannan kuma a kama shugabar kasar da ministocin tare da hukunta su kan zargin goyon bayan masu cin zarafin kananan yara.

Faya-fayan bidgiyo sun nuna yadda dubban mutane suka yi zaman dirshan a fadar shugabancin kasar, yayin da suka sha alwashin ci gaba da zama har sai Prime minister Viktor Orban ya bada umarnin kama mutanen.

 An dai zargi tsohuwar shugabar da goyon bayan masu cin zarafin kananan yara ta yadda ta iya yi musu afuwa bayan kamasu da laifin yiwa yaran da ke karkashin kulawar su fyade.

Tun wancan lokaci dai shugaba Novak ta musanta zargin, sai da bata bada dalilinta na yi musu afuwar ba, illa dai ta nemi afuwar al’ummar kasar wadanda basu ji dadin matakin da ta dauka ba.

Kididdiga ta nuna cewa wannan dambarwa ta yi awon gaba da kujerun kusoshin gwamnatin kasar 14.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.