Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Nijar ta yi gargadi game da tsoma bakin kasashen waje

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin Nijar a ranar Lahadi domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin da sojoji suka yi a watan da ya gabata, wanda shugabansu ya yi gargadi game da tsoma bakin kasashen waje yayin da yake bada shawarar mika mulki nan da shekaru uku masu zuwa.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani a yayin gabatar da jawabi ta talabijin ga al'ummar kasar game da rike mulkin na tsawon shekaru uku.
Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani a yayin gabatar da jawabi ta talabijin ga al'ummar kasar game da rike mulkin na tsawon shekaru uku. © AFP
Talla

Masu zanga-zangar  sun yi ta rera taken adawa ga Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka da kuma kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka, wadda ke nazarin yuwuwar yunkurin amfani da soja don maido da shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa, idan har tattaunawar da shugabannin da suka yi juyin mulki suka kasa cimma matsaya.

Wani bangare na masu zanga-zangar nuna goyon baya ga mulkin sojin Nijar a ranar Lahadi.
Wani bangare na masu zanga-zangar nuna goyon baya ga mulkin sojin Nijar a ranar Lahadi. REUTERS - STRINGER

Sabbin shugabannin gwamnatin sojin kasar da ke yankin Sahel sun haramta zanga-zanga a hukumance amma a aikace, masu goyon bayan juyin mulkin sun gudanar da ita.

Masu zanga-zangar sun daga allunan da ke cewa "A daina tsoma bakin soja" da "ba za mu lamunta da takunkumi ba", abin da ke nuni da batun rage tallafin kudi da takunkumin kasuwanci da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta sanya tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.

Taro na baya-bayan nan na juyin mulkin ya zo ne kwana guda bayan da sabon shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi gargadin cewa kutsen da sojojin kasashen waje ke yunkurin yi a Nijar ba zai haifar da 'da mai ido ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.