Isa ga babban shafi

Ana fuskantar zanga-zanga a yau ranar ma'aikata a fadin Duniya

Yayin da ake bikin ranar ma’aikata a yau Litinin a sassan duniya, shugaban Faransa, Emmanuel Macron, na fuskantar karin zanga-zanga a fadin kasar yayin da yake kokarin yiwa dokar fansho garambawul, abin da tayar da zaune tsaye, domin kuwa, a watan da ya gabata ne ya sanya hannu kan dokar da ta kara shekarun ritaya daga 62 zuwa 64, duk da yajin aikin da aka shafe watanni ana yi a kasar. 

Ma'aikata a kasar Morocco
Ma'aikata a kasar Morocco © Victor Mauriat/RFI
Talla

Macron da mukarrabansa tun a wancan lokaci suka yi kokarin samar da sauye-sauye kan lamarin da ya shafi walwalar jama’a, kuma batun na sauyin tsarin fansho na daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar wa’adinsa na biyu. 

Ma’aikata da masu fafutuka a fadin duniya na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar ma’aikata da aka saba yi duk ranar daya ga Mayu, inda suke kiraye-kirayen a kara musu albashi, da rage lokutan aiki da kyautata yanayin aiki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron gaban wasu ma'aikatan Faransa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron gaban wasu ma'aikatan Faransa AP - Christophe Petit Tesson

A Koriya ta Kudu, dubun-dubatar mutane ne suka halarci tarurruka daban-daban karon farko kenan, tun bayan barkewar cutar Covid-19.  

Mahalarta taron sun zargi gwamnatin shugaba Yoon Suk-yeol mai ra'ayin mazan jiya da durkusar da wasu kungiyoyin kwadago da sunan yin garambawul. 

A kasar Labanon, daruruwan 'yan jam'iyyar gurguzu da 'yan kasuwa, da kuma kungiyoyin ma'aikata, ne suka yi maci a kan titunan birnin Beirut. 

Wasu daga cikin ma'aikatan a kasar Lebanon
Wasu daga cikin ma'aikatan a kasar Lebanon AP - Hussein Malla

Sai dai a Pakistan, hukumomi sun hana gudanar da zanga-zanga a wasu garuruwa saboda matsalar tsaro. A Peshawar, dake arewa maso yammacin kasar, kungiyoyin kwadago sun gudanar da taron neman a inganta hakkin ma'aikata. 

Macin da aka yi a bana, an sami fitowar jama'a fiye da na shekarun da suka gabata, yayin da aka sassauta dokar kulle a kasashe da dama, inda masu fafutuka a sassan duniya, ke ci gaba da jan hankalin gwamnatoci kan muhimmancin inganta rayuwar ma’aikata. 

A kasar Taiwan, dubban ma'aikata ne suka fito kan tituna domin nuna adawa da abin da suka kira gazawar manufofin gwamnati a tsibirin mai cin gashin kansa, wanda ke matsa lamba ga jam'iyyar da ke mulki gabanin zaben shugaban kasa na 2024. 

Shugabar Tsibirin Taiwan Tsai Ing-wen, a wata liyafar cin abinci
Shugabar Tsibirin Taiwan Tsai Ing-wen, a wata liyafar cin abinci AP

Dubunnan mambobin kungiyar kwadago, 'yan adawa da masana ilimi sun hallara a filin taro na Yoyogi da ke Tokyo na kasar Japan, suna neman karin albashi don magance illar hauhawar farashin kayayyaki yayin da suka fara murmurewa daga kalubalen da annobar korona ta haifar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.