Isa ga babban shafi

Amurka ta bayyana shakkun shiga tattauna shirin nukiliyar Iran

Kasar Amurka tayi watsi da duk wani yunkuri na sake shiga tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran nan kusa, abinda ake gani zai dakushe fatar da ake da ita na kulla sabuwar yarjejeniya akan wadda akayi a shekarar 2015.

Shugaban Amurka kena Joe Biden
Shugaban Amurka kena Joe Biden © AP
Talla

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar John Kirby yace ba wai basa bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar bace, sai dai a halin yanzu basu ga wata hanyar kulla ta ba a nan kusa.

Kirby yace abinda ke gabansu yanzu shine daukar mataki akan kasar Iran saboda yadda take murkushe masu zanga zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka samu da laifin kin sanya hijabi a ranar 16 ga watan Satumba.

Mai magana da yawun fadar shugaban yace har yanzu shugaba Joe Biden na nan kan matsayinsa cewar ba zai taba barin kasar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Zanga zanga ta barke a sassan kasar tun bayan mutuwar Amini, abinda ya kaiga arangama tsakanin Yan Sanda da masu adawa da matakin da jami’an tsaro suka dauka, abinda ya kaiga mutuwar mutane sama da 100 da kuma kama wasu sama da 100 da tuni aka gurfanar a gaban shari’a.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya zargi Amurka da kawayenta da tinzira masu zanga zangar domin jefa kasar cikin tashin hankali, yayin da kasashen Turai suka amince da wani shirin kakabawa kasar takunkumi akan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.