Isa ga babban shafi
WTO

Za a fafata tsakanin Najeriya da Kenya a takarar shugabancin WTO

Tsohuwar ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala da ministan harkokin wajen Kenya Amina Muhammed na daga cikin sauran ‘yan takara 5 da suka rage cikin masu neman shugabancin Hukumar Kasuwanci ta duniya, WTO.

Hedikwatar Hukumar Kasuwanci ta duniya, WTO a birnin Geneva, dake kasar Switzerland.  2/6/2020.
Hedikwatar Hukumar Kasuwanci ta duniya, WTO a birnin Geneva, dake kasar Switzerland. 2/6/2020. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sauran sun hada da tsohon ministan tattalin arzikin Saudi Arabia Mohammed Maziad Al-Tuwaijri da tsohon ministan kasuwancin Birtaniya Liam Fox da kuma Yoo Myung-hee, tsohon ministan kasuwancin Japan.

Wakilan kasashen dake cikin kungiyar suka gudanar da tankade da rairaya inda suka sauke ‘yan takara guda 3 da suka hada da Jesus Seade na Mexico da Hamid Mamdouh na Masar da Tudor Ulianovschi na Maldova.

Shugaban taron kungiyar David Walker yace sauran ‘yan takara 5 da suka rage na da kwarewar da ake bukata wajen jagorancin Hukumar dake sanya ido kan harkokin kasuwanci na duniya.

Ana saran cigaba da tintiba tsakanin kasashen dake cikin kungiyar wajen ganin an rage ‘yan takarar zuwa guda 2 tsakanin 24 ga watan Satumba zuwa ranar 6 ga watan Okotbar wannan shekara.

Ana saran Hukumar ta samu sabon shugaba nan da ranar 7 ga watan Nuwamba.

A tarihin Hukumar ba’a taba samun wata mace ko kuma wani daga nahiyar Afirka da ya jagoranci Hukumar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.