Isa ga babban shafi
New Zealand

An tabbatar da mutuwar mutane 49 a harin Masallacin New Zealand

Mahukunta a birnin Christchurch na kasar New Zealand sun tabbatar da mutuwar mutane 49, bayan wani harin bindiga a masallatai biyu kan musulmai da ke tsaka da sallar Juma'a a yau, wanda kuma ya hallaka tarin jama'ar da ba a kammala gano adadinsu ba.

Hoton Masallacin Al Noor Mosque kenan da ke Christchurch na New Zealand
Hoton Masallacin Al Noor Mosque kenan da ke Christchurch na New Zealand Reuters/路透社
Talla

Harin wanda shi ne mafi muni da New Zealand ta taba fuskanta a tarihi tuni Firaminista Jacinda Ardern, ta bayyana shi da harin ta’addanci, inda ta sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu baya ga daukar matakan kare sake afkuwarsa a nan gaba.

Masallatan da aka kai harin sun hada da Masallacin Al-Noor mafi girma a birnin na Christchurch.

A wani faifan bidiyon harin an ga yadda maharan ke bin wadanda basu karasa mutuwa ba, suna karasa hallaka su, ciki har da wani matashi dan Australia mai shekaru 28 wanda tuni aka kame shi tare da wasu mutane 2.

Tuni dai gwamnatin New Zealand ta ce mutanen da ta kamen akalla 4 za su gurfana gaban kotun birnin na Christchurch a gobe Asabar don amsa tuhuma ka harin ta'addancin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.