Masar da Faransa sun fara wani hadin gwiwar atisayen Soji
Kasashen Masar da Faransa sun fara wani hadin gwiwar atisayen soji tsakanin kasashen a gabar tekun Méditerranéen, inda kasar masar za tayi gwajin jiragen yakin nan na Rafale Fighter jets da ta siyo daga Faransa.
Wallafawa ranar:
A tisayen da zai kwashe kwanaki ana yi zai gudana ne a gabar tekun Méditerranéen da ta ratsa garin Alexandria, a cewar dakarun masar.
Faransa dai ta ce zata shiga atisayen ne da jiragen ta samfurin Charles de Gaulle dake kaiwa mayakan IS hari a Syria da Iraqi, yayin da Rundunar sojin Masar tace jiragen ruwan yakin nan kirar Frigate da suma ta siya a Faransa za su shiga fagen.
A cewar ministan tsaro faransa atsisayen zai basu daman musayar dabarun fasahar yaki tunkarar ta’addanci.
A shekarar da ta gabata ne, Masar ta kula yarjejeniyar biliyoyin euro da Faransa wajen siyan jiragen yaki 24 wanda yanzu haka 6 sun isa kasar ta.
Atisayen kasashen biyu na zuwa yayin da kasashen yammacin ke cigaba da bayyana furgaban su dangane da karuwar mayakan IS a libya, kasar dake makawabtaka da Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu