Mutane 10 sun mutu a mummunan harin da aka kai a Istanbul
Akalla mutane 10 suka mutu yawancinsu Jamusawa a wani mummunan harin da wani dan kunar bakin wake da aka ce Dan Syria ne ya kai a birnin Istanbul na Turkiya.
Wallafawa ranar:
An kai harin ne a yankin Sultanahmet kusa da wani babban masallaci.
Akalla Jamusawa 9 ‘yan yawon bude ido aka kashe daga cikin mutane 10.
Sannan kimanin 15 suka jikkata a harin, yayin da rahotanni suka ce biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Yankin da aka kai harin wuri ne na tarihi da baki ‘yan kasashen waje ke kai ziyarar yawon bude ido.
Shugaban Turkiya Raceep Tayyib Erdogan, ya yi tir da harin, a jawabin da ya yi wa ‘yan kasar.
An danganta harin cikin munanan hare haren da aka taba ka iwa a Turkiya bayan harin watan Oktoba da aka kai a Ankara inda aka kashe mutane 103.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu