Kiristoci na bikin Kirsimeti a fadin duniya
Yau 25 ga watan Disemba mabiya addinin Kirista a sassan duniya ke gudanar da bikin Kirsimeti domin murnar tunawa da haihuwar Yesu da suke bautawa.
Wallafawa ranar:
A daren jiya jajibirin Kirsmetin an yi wasan wuta a manyan biranen kasashen duniya domin murnar zagayowar wannan rana.
A jawabinsa a jajibirin Kirsemeti Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Francis ya bukaci mabiya su rungumi rayuwa mai sauki, ba ta neman mallakar abin duniya ba.
Idan an jima a yau Juma’a Fafaroma zai gabatar da jawabin sakonsa na Kirismeti ga dimbin mabiya darikar katolika a filin st Peters a fadar Vatican.
Ana sa ran Fafaroma ya yi kira ga sasantawa da juna musamman a kasashen da ke fama da rikici.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu