Amurka-Rasha-Syria
Amurka ta ce Rasha ta tura jiragen yaki zuwa Syria
Kasar Amurka ta ce ko baya ga tankokin yaki da Russia ta tura zuwa Syria, har ila yau kasar ta tura jiragen yaki da dama domin bai wa shugaba Bashar Assad kariya.
Wallafawa ranar:
Talla
Zargin na Amurka dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ganawa tsakanin sakataren tsaron Amurka da kuma takwaransa na Rasha.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka Peter Cook ya ce a lokacin wannan ganawa, mutanen biyu sun amince za su ci gaba da yin aiki tare domin samar da mafita a game da rikicin kasar ta Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu