Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da Syria ta kai Turkiya

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da rokokin da dakarun kasar Syria suka harba cikin kasar Turkiya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar, cikinsu harda yara da mata. Harin dai ya jawo ramuwar gayya da kasar ta Turkiya ta yi akan kasar ta Syria wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu dakarun kasar. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon www.tunisiefocus
Talla

Majalisar ta yi Allah wadai ne da harin, a wata rubutacciyar sanarwa da ta fitar a jiya.

“Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausan suka da wannan hari da dakarun Syria su kai,” kamar yadda sanarwar ta nuna a rubuce.

Sanarwar dai ta fi mai da hankali ne wajen jan kunnuwan kasar Syria, kamar yadda Kamfanin Dillancin labarai na AFP ya rawaito, duk da cewa Turkiyan ta rama harin  bayan Syria ta bada hakuri.

Tuni dai Janar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Ban ki moon, ana shi bangare ya yi kira ga kasashen biyu da su sasantawa ta hanyar lumana.

“Janar Sakataren Majalisar na kira da ga duk bagarorin da su bi hanyar lumana wajen sasantawa.” Inji mai Magana da yawun Ban, Martin Nesirky.

Ban ya kuma kara nuna damuwarsa akan rikincin na Syria, inda yake nuna cewa zai iya watsuwa zuwa wasu sassa na Gabas ta Tsakiya.

Dama dai Majalisar ta taba magana akan yiwuwar rikicin na Syria ya watsu a yankin.

Harin akan kasar Turkiya wanda aka kai shi a ranar Larabar da ta gabata, shi ne na farko wanda ya yi sanadiyar mutuwar wata mata da ‘yayanta guda uku.

Kasar ta Turkiya dai ta rama harin, inda rahotanni ke nuna cewa dakarun kasar da dama sun mutu a harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.