Isa ga babban shafi
Rasha-Iran-Syria

Rasha ta amince da matakin kafa gwamnatin Riko a Syria

Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana goyan bayanta wajen ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta kunshi bangaren adawa da bangaren gwamnati a Syria, kamar yadda Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya bayyana.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha,  tare da Obama na Amurka
Shugaba Vladimir Putin na Rasha, tare da Obama na Amurka Reuters
Talla

Wannan kuma na zuwa ne bayan Kofi Annan yace za su amince da kasar Iran cikin tawagar kasashen da ke kokarin kawo karshen rikicin Syria kamar yadda Rasha ta bukata duk da cewa ba a gayyaci Iran ba domin tattauna batun ba.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Martin Nesirky yace Kofi Annan zai tattauna da kasar Iran bayan taron Ministocin waje da za’a yi a Geneva game da batun rikicin kasar Syria.

Rusha da kasar Iran sun kasance kawayen kasar Syria da suka rage, masu goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad tun fara boren neman kawar da shi daga madafun ikon kasar watanni 15 da suka gabata.

Sai dai Kasar Amurka da kasashen Turai sun soki batun shigar da kasar Iran domin sasanta rikicin kasar ta Syria.

Amma Har yanzu Kasar Iran bata ce komi ba game da kin gayyatar ta a taron Geneva game da Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.