Isa ga babban shafi
Philippines

An Jana’izar wadanda suka mutu a Philippine

A kasar Philippine masu aikin ceto sun yi jana’iza ta bai-daya ga wadanda suka mutu, sakamakon ambaliyar ruwa da iska mai tsanani da suka shafi wasu yankunan kasar. Matsalar ta faru ne tun lokacin da masu hasashen yanayi suka garagadi mazauna yankunan Cagayan, kan ficewa daga kauyukansu, saboda yiwuwar fuskantar ambaliya a ranar Assabar, inda kuma suka yi watsi da wannan gargadin, lamarin da yasa ambaliyar da afka musu ba zato ba tsammani.

Wasu da Ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Philippines
Wasu da Ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Philippines Reuters
Talla

Har zuwa jiya Lahadi, masu aiki ceto, sun ci gaba da zakulo gawarwakin mutanen da suka mutu, tare da ceto wadanda suka tsira da ransu.

A jiyan an ga gawawwaki da dama suna yawo kan ruwa, inda da tuni wasu suka rube, suna wari, abin da ya jefa masu aikin ceton cikin wani hali.

A halin yanzu, an tabbatar da mutuwar kusan mutane 700, yayin da wasu kusan 900 suka bace.

An yi jana’iazar mamatan ta bai-daya, kuma Sakatare janar na kungiyar agaji ta Red Cross a kasar, Gwendolyn Pang yace za’a sa alamu kan kaburburan mamatan, tare da daukar hotuna domin Shaida su a nan gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.