Isa ga babban shafi
Indonesia

Ziyarar Obama a Indonisiya

A ziyararsa ta kwanaki goma yankin Asiya, Shugaba Obama a yau talata ya sauka kasar Indonisiya, a wani kawance da shugaban ke neman kullawa da kasar kan harakokin kasuwanci da ci gaban demokradiyya. A daidai wannan lokacin Obama na ziyartar kasar ne a matsayin ziyartar gida, bayan da shugaban ya kwashe shekaru hudu yana zaune a kasar lokacin da yana yaro.

Shugaba Obama da Shugaban kasar Indonisiya Susilo Bambang Yudhoyono a Jakarta
Shugaba Obama da Shugaban kasar Indonisiya Susilo Bambang Yudhoyono a Jakarta Photo: Reuters
Talla

Ziyarar Obama zuwa kasar wacce tafi kowacce kasa yawan musulmi a duniya da kuma a yanzu haka ke cikin zullumi na bala’in da ya aukawa kasar na aman wutar dutsin Marapi a kwanan baya.

00:10

Amirka zata karfafa zumunci da musulmin duniya

Shugaban a yau, ya bayyana irin ci gaban da kasar ta samu na fita daga mulkin danniya zuwa mulkin demokradiyya, inda Amurka ta taimaka wajen bunkasa kungiyoyin fararen hula wajen yaki da keta hakkin Bil’adama da kuma cin hanci da karbar rashawa a kasar.

A gobe ne dai ake sa ran shugaban zai kai ziyara manyan masallatan kasar da suka hada da masallcin Itiqlal, masallaci mafi girma a kudu maso gabacin Asiya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.