Isa ga babban shafi
Iran

Kasar Iran za ta jinkirta tattaunawa da kasashen yamma kan shirinta na Nukiliya

Kasar Iran ta ce za ta jinkirta tattaunawa da kasashen yamma kan shirinta na Nukiliya har sai karshen watan Agusta, don ta ladabtar da su.Da yake sanar da hakan yau a Tehran, shugaban kasar Mahmoud Ahamadinejad ya yi kiran da a sami karin kasashe da zasu shiga maganar.Ahmadinejad ya ce za a iya cim ma yarjejeniya da kasarsa kan shirinta na Nukiliya daga bayan tsakiyar watan Ramadan zuwa karshen watan Agusta, ya na mai cewa ya kamata kasashen yamma su koyi yadda zasu rika hulda da kasashe.Wadannan kalamai nasa martani ne ga karin takumkumi da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kakaba wa Iran, ranar tara ga watan nan, bayan da ta ci gaba da inganta sanadarinta na Yuraniyam.  

Shugaban kasar Iran Amadinejad ke jawabi ga manema labarai a Tehran
Shugaban kasar Iran Amadinejad ke jawabi ga manema labarai a Tehran Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.