Isa ga babban shafi
Russia

Jakadan kasar Rasha a kungiyar tarayyar Turai ya yi Allah wadai da sanya wa Iran takunkumi

Yau juma’a ne jakadan kasar Rasha a kungiyar tarayyar Turai ya yi tofin Alla-tsine ga yadda Amurka da kuma kungiyar tarayyar Turai suka yanke shawarar kakaba wa kasar Iran takunkumi, dangane da shirinta na Nukiliya.Ya kuma ce ahir kada wannan mataki ya kuskura ya shafi kamfanoni ko kuma huldodin kasar ta Rasha.Vladimir Chizhov ya kara da cewa kakaba wa Iran takunkumi na Mai da kuma Iskar gas ya saba wa matakan majalisar dinkin duniya, wadanda Mascow ke goyon baya.Bama goyon bayansu, muna ganin sun tafka babban kuskure a tunaninsu da kuma aiwatar da wannan manufa, a ta cewarsa.  

Shugaban kasar Rasha Medvedev
Shugaban kasar Rasha Medvedev © REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.