Isa ga babban shafi

An ceto fasinjojin da suka makale a motar kebur a Pakistan

Jiragen soji masu saukar ungulu tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 8, ciki har da kanan yara ‘yan makaranta 6, wadanda suke cikin wata mota mai tafiya a waya, wanda ya makale a bisa wani kwari da ke wani kauye a kasar Pakistan a ranar Talata.

Hotunan da aka dauko na motar sama da taa  makale a bisan wani kwari a Pakistan dauke da wasu mutane 8 ciki har da yara 6.
Hotunan da aka dauko na motar sama da taa makale a bisan wani kwari a Pakistan dauke da wasu mutane 8 ciki har da yara 6. AP
Talla

Sai da aka shafe sa’o’i 12 ana ta wannan aikin ceto da jirgi mai saukar ungulu sannan aka ceto yaro guda, kuma bayan ceton ne ya zama tilas ma’aikatan su koma sansaninsu sakamakon mummunan yanayi da kuma karatowar dare.

Daga bisani dakarun na musamman da ake wa lakabi da Maroon Barets sun yi amfani da dabaru na kwararru wajen ceto wadannan fasinjoji da suka makale a wannan mota.

Wasu daga cikin yaran da aka ceto sun shaida wa Kaamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, sun zata kwanansu ya kare, inda suka mika godiya da abin da suka kira  "lokaci da aka sake ara  musu".

Firaminstan Pakistan mai rikon kwarya, Anwar ul-Haq Kakar ya  bayyana masu aikin ceton a matsayin gwaraza na kasar.

‘Yan uwa da abokan wadanda suka tsinci kansu a cikin wannan jarabawa sun yi ta rungumar su cikin hawaye na farin ciki bayan da aka kammala aikin ceton. A yayin wannan aiki na ceton fasinjojin wannan mota, dimbim mutanen da suka taru sun yi ta addu’o’i sakamakon fargabar da suke da ita a game  kan yiwuwar tsinkewar igiyar da ta rike motar.

Yara shidan, da wasu manya biyu da ke musu rakiya zuwa makaranta ne suka gamu da wannan jarabawa  da misalin karfe 7 na safe, wato karfe 2 agogon GMT.

Mutanen yankin su yi ta yekuwa ta wajen amfani da amsar kuwwar masallaci don ankarar da hukumomin da abin ya shafa a game da makalewar da motar ta  yi.

A shekarar 2017, mutane 10 ne suka mutu a yayin da irin wannan motar ta fado bayan da wayar da ke rike da ita ta tsinke a kusa da babban birnin kasar Islamabad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.