Isa ga babban shafi

Jam'iyyar adawa ta Thailand na shirin karbe mulki daga hannun sojoji

Babbar jam’iyyar adawa a Thailand, wato Move Forward MFP a takaice, ta yi ikirarin lashe babban zaben kasar, jim kadan bayan da sakamakon kuri’un da aka kada ya  nuna cewar, jam’iyyar ta yi wa sauran takwarorinta da sojoji ke marawa baya fintinkau. 

Pita Limjaroenrat, shugaban Jam'iyyar Move Forward da magoya bayansa.
Pita Limjaroenrat, shugaban Jam'iyyar Move Forward da magoya bayansa. AP - Sakchai Lalit
Talla

Zaben na Thailand da ya gudana a ranar Lahadi ya kawo karshen kusan shekaru 10 da kwancen jam’iyyu masu barin gado suka shafe suna mulkin kasar. 

A halin yanzu MFP mai jiran gado na gaf da zama jam’iyya mafi girma a Thailand, biye da ita kuma jam’iyyar ‘Pheu Thai’ da ke karkashin jagorancin hamshakin attajirin kasar kuma tsohon Firaminista Thaksin Shinawatra. 

Jagorar MFP Pita Limjaroenrat ya ce zai kafa gwamnatin hadin-guiwa da za ta kunshi kawancen jam’iyyu shida, ciki kuwa har da ta Pheu Thai ta tsohon Fira Minista Shinawatra, sai dai bai tsayar da lokaccin fara tattauna wa ba. 

Kafin zaben da ya bai wa jam’iyyar MFP gagarumin rinjaye, Firaminista Prayut Chan-O-Cha ya sha caccaka a bisa zargin sa da gazawa wajen kawo karshen kalubalen karayar tattalin arzikin da Thailand ke fuskanta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.