Tsare Imran Khan ya saba ka'ida - Kotun Kolin Pakistan
Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan da ke tsare zai gurfana a gaban kotu wannan Jumma’a, bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukuncin cewa kamen da aka yi masa ya a karshen mako wanda ya haifar da kazamin rikici tsakanin magoya bayansa da jami’an tsaro ya saba ka'ida.
Wallafawa ranar:
Alkalin kotun Umar Ata Bandial ya shaida wa Khan a wani zaman sauraren karar da aka yi a Islamabad babban birnin kasar ranar Alhamis cewa: Kamun da aka yi masa bai dace ba, don haka dole a sake tsarin kamen.
An umurci Khan da ya ci gaba da zama a bayan kanta karkashin kariyar ‘yan sanda don kare lafiyarsa har zuwa yau Juma’a da za a bayyana a kotu.
Sake kama shi
Sai dai gwamnati ta sha alwashin sake kame Khan idan aka sake shi, lamarin da ake fargabar zai sake rura wutan rikici a kasar.
Tun bayan hambarar da shi daga mukaminsa a watan Afrilun da ya gabata, Khan ya gudanar da yakin neman zabe mai tsauri tare da yin suka da ba a taba ganin irinsa ba ga shugabannin Pakistan da manyan sojoji masu karfin fada aji.
Ya zarge su da shirya wani yunkurin kashe shi a watan Nuwamba da ya sa aka harbe shi a kafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu