Isa ga babban shafi

Kotun Sojin Myanmar ta karawa Aung San Suu Kyi shekaru 7 na zama a yari

Kotun Soji a Myanmar ta sake yanke hukuncin karin shekaru 7 ga tsohuwar hambararriyar shugabar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi matakin da ya mayar da yawan shekarun da za ta yi a kaso zuwa 33.

Aung San Suu Kyi, hambararriyar shugabar gwamnatin Myanmar.
Aung San Suu Kyi, hambararriyar shugabar gwamnatin Myanmar. AP - Wason Wanichakorn
Talla

Tsohuwar shugabar na fuskantar tsarewar gida ne tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da ita a watan Fabarairun 2021 inda aka shafe watanni 18 ana tuhumarta kan laifuka 19 da ake zarginta da aikatawa ciki har da cin amanar kasa.  

Ko a makon jiya sai da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sakinta yayinda kungiyoyin kare hakkin dan adam ke ci gaba da kiraye-kirayen ganin an sako ta.

Yayin shari’ar ta yau juma’a da ke matsayin ta karshe, kotun Sojin ta samu tsohuwar jagorar da dukkanin laifukan da ake zarginta da aikatawa musamman ta yadda ta gaza bin ka’ida wajen hayar jirgin Shalkwafta ga guda cikin ministocinta.

Kafin shari’ar ta yau da ta kai ga karin hukuncin shekaru 7 ga Aung San Suu Kyi, dama tuni ta amsa laifuka 14 da ake tuhumarta ciki har da karya dokokin kulle yayin annobar Covid-19 sai kuma mallakar na’urar magana ta tafi da gidanka da kuma daukar matakai a boye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.