Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 22 a kasar Iran
Akalla mutane 22 ne ambaliyar ruwa ta kashe a kudancin Iran, yayin da mutum daya ya bace, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar.
Wallafawa ranar:
Iran ta sha fama da fari a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da a hannu guda take fama da ambaliya a kai a kai, masamman lokacin saukar ruwan sama.
Hotunan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna yadda kogin Roodball da ya cika ya batse a lardin Fars da ke kudancin kasar ke tafiya da motaci.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda aka ciro wani yaro daga mota da ruwa ke kokarin janyewa .
Tun da farko wani jami'in kungiyar agaji ta Red Crescent ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 21, yayin da wasu mutane biyu suka bace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu