Isa ga babban shafi

Shugaban Sri Lanka zai yi murabus bayan masu zanga-zanga sun sa ya tsere

hugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa yana shirin yin murabus a Lahadin nan bayan da masu zanga zanga suka tilasta masa tserewa daga gidansa a jiya Asabar.

Shugaban Sri Lanka  Gotabaya Rajapaksasa ya ce zai yi murabus.
Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksasa ya ce zai yi murabus. AFP/File
Talla

Lamarin na Asabar ya auku ne sakamakon matsin tattalin arziki da al’ummar kasar suka fada ciki, lamarin da ya harzuka su har suka shiga zanga zanga.

Dubban masu zanga zanga ne suka taru a babban birnin kasar Colombo don nuna rashin amincewar su da abin da suka kira matsalar tattalin arziki irin wadda ba su taba gani ba, wadda suka zargi gwamnatin kasar da haddasawa.

Bayan da suka afka cikin gidan shugaban kasar, masu zanga zangar sun shiga daki daki na fadar, inda har wasu daga cikinsu suka fada cikin kududdufin ninkaya da ke harabar fadar.

Bayan haka ne kakakin fadar shugaban kasar, Mahinda Abeywardana ya fitar da wata sanarwa da ke cewa shugaban ya yanke shawarar rabuwa da kwallon magwaro don ya huta da kuda a ranar 13 ga watan Yulin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.