Isa ga babban shafi
Isra'ila-Rasha

Isra'ila ta bukaci Rasha ta nemi afuwa a kan danganta Hitler da Yahudawa

Isra’ila ta bukaci Rasha ta nemi afuwarta biyo bayan kalaman ministan harkokin wajen Rasha da ya danganta mutumin da ya haddasa yakin duniya na 2, wato Adolph Hitler da kasar ta Yahudawa.

Firaministan Isra'ila Naftali Bennett.
Firaministan Isra'ila Naftali Bennett. AP - Sebastian Scheiner
Talla

A ganawa da ya yi da wata kafar talabijin Italiya a ranar Lahadi, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov  ya ce yana da yakini cewa Adolph Hitler daga tsatson Yahudawa ne.

Kalaman Lavrov sun zo ne bayan da aka tambaye shi ta yaya Rasha za ta ce tana wanke akidar Nazi daga kwakwalen ‘yan Ukraine, alhalin kuwa shugaba Volodymyr Zelenskyy Bayahude ne.

Lavrov ya ce sunshafe tsawon lokaci suna jin cewa ai babu wadanda suka yi wa yahudawa kisan kare dangi kamar su Yahudawan da kansu.

fiora ministan Isra’ila Naftali bennett ya yi watsi da kalaman, yana mai cewa dole a daina amfani da batun kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawa a a matsayin wani makami na siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.