Isa ga babban shafi
India

Barayi sun sace gada mai tsawon kafa 60 a kasar India

A wani yanayi mai kama da almara a kasar India, wata kungiyar barayi ta sace gada mai tsawon kafa 60 ta hanyar kwance karafunan da aka gina ta da shi mai nauyin tan 500 inda suka gudu da shi.

Wani mutum yana tafiya a kan wata gada da ta haɗu Myanmar da Indiya a ƙauyen Zokhawthar da ke kan iyaka, gundumar Champai, a Mizoram na Indiya, Maris 12, 2021.
Wani mutum yana tafiya a kan wata gada da ta haɗu Myanmar da Indiya a ƙauyen Zokhawthar da ke kan iyaka, gundumar Champai, a Mizoram na Indiya, Maris 12, 2021. © REUTERS/Rupak De Chowdhuri/Files
Talla

Baturen ‘Yan Sandan Yankin dake Jihar Bihar, Subash Kumar ya bayyana cewar barayin sun je yankin ne da sunan jami’an kula da noman rani na gwamnati dauke da manyan motoci da kuma na’urorin yanka karafa, inda suka kwashe kwanaki biyu suna kwance karafunan da akayi gadan shi kafin su gudu da shi.

Kumar yace barayin sun kwashe kwanaki biyu suna aikin kwance gadar da ta kwashe shekaru 50 da ginawa ba tare da mutane sun ankara ba, yayin da suka yi amfani da wata babbar mota wajen gudu da karafunan.

Ya zuwa yanzu dai ‘Yan Sandan sun kaddamar da bincike akan lamarin ba tare da kama koda mutum guda daga cikin tawagar barayin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.