Isa ga babban shafi
Bangladesh

Mutane da dama sun bace a Bangladesh bayan nutsewar wani jirgin ruwa

Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan aka yi amannar bacewar wasu da dama bayan da wani jirgin ruwan dakon kaya ya afka wani karamin jirgin daukar fasinja a wani kogi kusa da babban birnin Bangladesh.

Hadarin jiragen ruwa ya hallaka mutane 5 a kasar Bangladesh, ranar 20/03/2022.
Hadarin jiragen ruwa ya hallaka mutane 5 a kasar Bangladesh, ranar 20/03/2022. © AFP
Talla

'Yan sanda sun ce kusan mutane goma sha biyu ne suka kubuta bayan da suka yi iyo a gabar tekun da ke kudu maso gabashin Dhaka.

Hotunan nutsewar da kafafen yada labarai na kasar suka nuna sun nuna yadda mutane ke ta kururuwa cikin fargaba yayin da jirgin dakon kaya ya yi karo da karamin jirgin da ya nutse cikin sauri.

“Mun gano gawarwaki biyar da suka hada da mutum daya da mata uku da yaro daya,” kamar yadda shugaban ‘yan sandan yankin Shah Jaman ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

An yi imanin cewa jirgin yana dauke da fasinjoji sama da 60 kuma 22 daga cikinsu sun yi iyo a gabar tekun su fita lami lafiya, in ji sufeto 'yan sanda Aslam Mia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.