Isa ga babban shafi
MDD-China

Guterres ya nemi China ta bai wa shugabar kare hakki damar shiga Xinjiang

Babban sakateren Majalisar Dinkin Duniya  Antonio Guterres ya shaida wa jagororin China cewa kamata ya yi su bari shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar Michelle Bachelet ta kai wata ziyara mai mahimmanci kasar, tare da yada zango a yankin Xinjiang mai fama da rikici.

Sataren majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Sataren majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres. Fabrice COFFRINI AFP/Archivos
Talla

Guterres ya gana da shugaban China Xi Jinping da kuma ministan harkokin wajen kasar bayan da aka soma gasar wasannin Olympics ta bazara.

 Sanarwar bayan ganawar tasu ba ta yi magana a game da  matsalar hakkin dan adam ba.

Masu rajin kare hakkin dan adam sun ce akalla Musulmai miliyan 1 ne hukumomin China suka garkame a sansanonin da suka kira jaddada ilimi a yankinn yammacin kasar, inda ake zargin hukumomi da keta haddin dan adam, ciki har da tirsasa wa mata karbar allurar hana daukar ciki da sa maza aikin dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.