Isa ga babban shafi
Indonesia-Malaysia

'Yan ci-rani 11 sun mutu a tekun Malaysia

Akalla ‘yan ci-ranin Indonesia 11 ne suka rasa rayukansu, 25 suka bace sakamkon kifewar kwale-kwalensu a gabar ruwan Malaysia a yau Laraba.

EUROPE-MIGRANTS/FRANCE-CALAIS
EUROPE-MIGRANTS/FRANCE-CALAIS © REUTERS - POOL
Talla

Mutanen Indonesia da ke neman aiki na yin  balaguro zuwa Malaysia mai makwabtaka da su ta barauniyar hanya, inda suke kasadar ratsawa ta teku a cikin kananan jiragen ruwa.

Ana yawan samun haduurran kananan jiragen ruwan a wannan teku kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Hatsarin baya-bayan nan ya auku ne a yayin da jirgen ruwan ke dauke da mutane 50 a cikinsa, yayin da sojoji suka kwaso gawarwakin mutanen da suka nutse.

Rahotanni na cewa, an yi nasarar ceto wasu karin mutane 14 da ransu.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.