Isa ga babban shafi
Indonesia

Aman wutar tsauni ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 10 a Indonesia

Adadin wadanda suka mutu sakamakon aman wutar da tsaunin Semeru na kasar Indonesiya ya yi, ya kai mutane 13, yayin da masu aikin ceto ke cigaba da binciken kauyukan toka ta lullube da fatan gano wasu da suka saura da ransu.

Yadda iftila'in aman wuta daga tsaunin Semeru a tsibirin Java na kasar Indonesia ya haifar rushewar gine-gine da dama, ciki har da wata gada da ta rushe a yankin.
Yadda iftila'in aman wuta daga tsaunin Semeru a tsibirin Java na kasar Indonesia ya haifar rushewar gine-gine da dama, ciki har da wata gada da ta rushe a yankin. via REUTERS - ANTARA FOTO
Talla

Akalla mutane 57 suka jikkata sakamakon iftila’in kuma 41 daga cikinsu sun samu raunuka ne na kuna.

Aman wutar da tsaunin na Semeru mafi girma a tsibirin Java yayi, ya zuwa al’ummar yankin cikin bazata a jiya Asabar, lamarin da ya tilastawa daruruwan mutane gudun hijira daga muhallansu.

Aman wutar tsaunin dai ya lalata akalla kauyuka 11 na gundumar Lumajang, tare da raba mutane 900 da muhallansu.

Sakamakon wani binciken kwararru ya tabbatar da cewa Indonesia ta fi kowace kasa fuskantar hatsarin aukuwar girgizar kasa, da aman wuta daga tsaunuka, da kuma ambaliya ruwa, kasancewar ta a yankin Pacific, wadda daga karkashinsa aka fi samun yawaitar motsawar kasa.

A shekarar 2004, wata gagarumar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 a ma’aunin Richter ta haddasa daga yankin Sumatra dake yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar rayukan mutane akalla dubu 220,000 da ke zaune a yankunan da ke gaf da tekun India, kuma dubu 168,000 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.