Isa ga babban shafi
Qatar

Bakin-haure 50 dake kwadago a Qatar ne suka mutu a 2020

‘Yan cirani da ke aikin kwadago hamsin ne suka mutu a Qatar a bara sannan sama da 500 sun samu munanan raunuka, a daidai lokacin da kasar ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.

Rahoton na zuwa ne a yyin da ake caccakar yanayin da ma'aikata baki ke aiki a Qatar.
Rahoton na zuwa ne a yyin da ake caccakar yanayin da ma'aikata baki ke aiki a Qatar. © Kai Pfaffenbach / Reuters
Talla

Rahoton da kungiyar kwadago ta duniya ta fitar, ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar yanayin aiki ga dubun dubatar ma'aikata bakin haure, ciki har da wadanda suka gina filayen wasa don gasar cin kofin duniya.

Rahoton , ya ce babban abin da ya fi haifar da hakan shine faduwa daga saman gini, ko kuma zubewar gini ko kuma wani abu na daban a kan su. Kuma galibi wadanda abin ya fi shafa sun fito ne daga kasashen, Bangladesh, India da Nepal.

Qatar, wadda ta yi jerin sauye sauye a bangaren kwadagonta, da suka hada da bullo da tsarin mafi karancin albashi na dala 275 duk wata da kuma saukaka hanyar canjin wajen aiki tun da aka zabe ta a matsayin wadda za ta dau nauyin gasar cin kofin duniya ta 2022, ta yi na’am da rahoton, inda ta ce tana matukar daraja dangantakarta da kungiyar kwadago ta duniya ILO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.