Isa ga babban shafi
Aghanistan - Faransa

Faransa ta bukaci 'yan kasarta su fitce daga Afghanistan

A yayin da fafatawa ke kara ta'azzara tsakanin sojojin gwamnti da mayakan Taliban a kasar Afghanistan,  Faransa ta bukaci daukacin 'Yan kasar ta dake Afghanistan da su gaggauta ficewa daga cikin kasar, ganin yadda mayakan Taliban suka kaddamar da hare hare masu zafi da zummar karbe iko da kasar baki daya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin wani jawabi ta hoton bidiyo 25 ga watan Janairu 2021.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin wani jawabi ta hoton bidiyo 25 ga watan Janairu 2021. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Wata sanarwar da ofishin Jakadancin kasar ya aikewa mazauan kasar ta bayya shirya jirgin sama da zai kwashe Yan kasar daga Kabul zuwa gida kyauta ranar Asabar mai zuwa.

Ofishin Jakadancin yace ba zai iya tabbatar da kariyar Yan kasar ba bayan 17 ga wannan wata na Yuli.

Tuni kungiyar Taliban ta yi ikirarin kwace iko da yankin Spin Baldok mai muhimmaci dake iyaka da Pakistan a wannan Laraba, a dai-dai lokacin da suke kokarin kutsa kai da kwace babban birnin Kabul, inda suka bukaci gwamnati da ta mika wuya don gudun zubur da jini a birnin.

Ko daya yake gwamnatin kasar Afghanistan ta bakin ministan cikin gida, ta ce har yanzu ita ke rike da birnin sabanin ikirarin Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.