Isa ga babban shafi
Jordan-Masarauta

Sarkin Jordan ya amince ya sulhunta da Yarima Hamzah

Sarki Abdallah na Jordan ya amince ya yi sulhu a cikin gida da dan uwansa Yarima Hamzah da aka zarga da yunkurin kifar da gwamnatinsa, aka kuma masa daurin talala.

Sarkin Jordan Abdallah na biyu da Yarima Hamzah da wasu 'yan gidan sarautar kasar
Sarkin Jordan Abdallah na biyu da Yarima Hamzah da wasu 'yan gidan sarautar kasar © Khalil Mazraawi/ Getty Images/ AFP
Talla

Gwamnatin Jordan ta zargi Yarima Hamza, wanda tsohon mai jiran gadon Saratar kasar ne, da hada baki domin haifar da matsalar tsaro a kasar, abin da ya sa aka tsare shi tare da wasu mutane 16.

Fadar Sarkin ta ce Abdallah ya yanke hukuncin fuskantar matsalar ta Yarima Hamzah ta bangaren cikin gidan Sarautar Hashemite kuma ya mika wa kawunsa Yarima Hassan ragamar sasanta lamarin.

Kafin dai hakan, Yarima Hamzah ya ce ba zai yi biyayya ga wani umurni daga fadar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.