Isa ga babban shafi
Coronavirus

Adadin wadanda cutar korona ta kashe a Gabas ta Tsakiya ya haura dubu 100

Hukumar Lafiya ta Duniya tace mutanen da cutar korona ta kashe a Gabas ta Tsakiya sun zarce 100,000 daga cikin mutane kusan miliyan 5 da suka harbu da cutar tun bayan barkewar ta a watan Nuwambar bara.

Ma'aikatar kiwon lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona wuhan
Ma'aikatar kiwon lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona wuhan Hector RETAMAL / AFP
Talla

Wannan ya sanya Yankin a matsayin na 5 daga cikin yankunan duniya da suka fuskanci annobar, bayan Ynakin Turai da aka samu mutane 789,310 da suka mutu, sai Yankin kudancin Amurka mai mutane 628,398 sai Amurka mai mutane 492,313 sannan Asia mai mutane 245,899.

A mako guda da ta gabata, an samu akalla mutane 25,114 da suke kamuwa da cutar kusan kowacce rana, yayin adadin masu mutuwa ya ragu zuwa 238 kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.