Kyrgystan ta samu sabon Firaminista
Majalisar Dokokin Kyrgystan ta zabi Sadyr Japarov a matsayin sabon Faranminista, bayan da shugaban gwamntin kasar Koubatbek Boronov ya yi murabus biyo bayan zanga-zangar adawa da sakamkon zabe.
Wallafawa ranar:
Majalisar wadda ta sanar da zaben sabon Franministan ta ce matakin ya samo asali ne yayin taron gaggawa na musamman da ta yi a wannan Talatar bayan murabus din shugaban gwamnati Koubatbek Boronov, mai samun goyan bayan shugaban kasa mai ci.
A cewar sashin labarai na majalisar, an gudanar da taron gaggawar da ya kai ga zaben sabon Franministan Sadyr Japarov ne, a wani otel saboda masu zanga-zanga sun ci gaba da mamaye majalisar dokokin kasar.
Rahotanni sun ce, mutumin da aka zaba a matsayin sabon shugaban gwamnati na daya daga cikin fursunoni da masu zanga-zangar adawa da sakamakon zabe suka kubutar lokacin da suka kwace gine-gine gwamnati, cikin su har da tsohon shugaban kasa Almazbek Atambayev.
Tuni Hukumar zaben Kyrgystan ta sanar da soke zaben ‘yan Majalisun da aka yi a karshen mako saboda zanga zangar adawa da sakamakon sa wanda ke neman jefa kasar cikin tashin hankali.
Yayin da jiga-jigan 'yan adawar kasar cikinsu har da tsohon Firaminista da suka soki sakamakon zaben inda suka sanar da kafa kungiyar da za ta tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar.
A halin da ake ciki rahotanni sun tabbatar da cewar, shi kansa shugaban kasar Kyrgyzstan da ke cikin rudani ya bayyana cewa a shirye ya ke ya sauka domin mika mulki ga wani jigon siyasa da bai bayyana kowane ne shi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu