Isa ga babban shafi
New Zealand

Hada-hada ta dawo a New Zealand bayan warkewar ilahirin masu corona

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta sanar da janye ilahirin dokokin da ta sanya don hana yaduwar COVID-19 bayan shafe makwanni 2 ba tare da samun ko da mutum guda da ya kamu da cutar ba, haka zalika babu wani majinyaci da yanzu haka ke kwance a asibiti sanadiyyar coronavirus.

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern.
Firaministar New Zealand Jacinda Ardern. REUTERS/Martin Hunter
Talla

A jawabin da ta gabatar gaban manema labarai, Firaminista Arden, ta ce daga yanzu babu hani kan taruwar jama’a duk yawansu, haka zalika dukkanin makarantu, wuraren ibada da sauran wuraren shakatawa da shagunan cinikayya za su ci gaba da kasancewa a bude.

Sai dai Firaminista Arden, ta ce har yanzu ilahirin iyakokin kasar za su ci gaba da kasancewa a kulle don gudun shigo musu da cutar ta coronavirus daga ketare.

Acewar Firaminsitar yanzu kasar ba ta cikin hadarin cutar sai dai ya zame musu wajibi karawa bangaren lafiyarsu kasafi mai yawa don tunkarar annoba makamanciyar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.