Isa ga babban shafi
China-Corona

Xi ya nemi baiwa likitoci cikakkiyar kariya bayan corona ta kashe 7

Shugaban China Xi Jinping ya bukaci daukar sabbin matakan kariya kan jami’an lafiyar da ke kula da masu dauke da cutar corona bayan mutuwar wani fitaccen Likita da ya harzuka al’ummar kasar inda suke zargin gwamnati da gazawa wajen yaki da cutar.

Shugaban China Xi Jinping a ziyarar da ya kai yankin da cutar corona ta tsananta.
Shugaban China Xi Jinping a ziyarar da ya kai yankin da cutar corona ta tsananta. Xinhua via REUTERS ATTENTION EDITORS
Talla

Kawo yanzu jami’an lafiya 7 ne suka mutu cikin kusan dubu 1 da 716 da aka gwada sun kamu da cutar ta coronavirus ko kuma COVID-19 a kokarinsu na kula da marasa lafiya galibinsu a Lardin Hubei, matakin da yanzu haka ya harzuka al’ummar kasar tare da bore ga gwamnati don nuna gazawarta wajen yaki da cutar.

Wasu jami’an sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP yadda suke fuskantar karancin kayakin kariya daga cutar, ciki har da mayanin kulle hancin da rigunan shiga wajen masu dauke da cutar don duba lafiyarsu.

Wasu majiyoyi sun bayyana yadda jami’an lafiyar kan ci gaba da duba lafiyar majinyatan duk da yadda alamomin cutar ya fara bayyana a tare da su, yayinda a bangare guda tarin jami’an lafiyar kan yi amfani da rigar kariya daga cutar guda daya tal, ta yadda sai wani ya cire kana wani yayi amfani da ita.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ruwaito shugaba Xi Jinping na cewa ya zama wajibi a wadata jami’an lafiyar da kayakin da ke bukata tare da karfafa musu gwiwa don basu damar ci gaba da aiki tukuru wajen yakar cutar.

Mutuwar Liu Zhiming babban daraktan Asibitin Wuchang na yankin Wuhan a lardin Hubei a jiya Talata mako guda bayan mutuwar Li Wenliang a yanki guda ya darsa zargi a zukatan al’ummar kasar na cewa gwamnati bata daukar matakan da ya dace wajen yaki da cutar.

Wata majiya ta bayyana cewa yanzu haka akwai karin jami’an lafiya dubu 1 da 300 da ake kyautata zaton suma sun kamu da cutar ta corona dai dai lokacin da adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai dubu 74 da 185 inda ake da jumullar mutane dubu 2 da cutar ta kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.