Isa ga babban shafi

Masu zanga-zangar Lebanon sun sake tururawa duk da farmakarsu

Dubbunnan masu zanga-zanga sun sake bazuwa a tsakiyar Birnin Beirut yau Talata duk da barazanar kungiyoyin shi’a na Amal da Hezbollah wadanda suka farmaki masu zanga-zangar tsakaddare.

Wasi masu zanga-zanga a Lebanon.
Wasi masu zanga-zanga a Lebanon. REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Zanga-zangar wadda ta tsananta bayan kiran Majalisar Dinkin Duniya na ganin an gudanar da ita a tsanake maimakon kone-kone da ta’adin da ke kaiwa ga rasa rayuka, inda mashirya zanga-zangar suka bukaci gudanar da gangami mafi girma.

Gabanin harin na tsakaddaren Lahadi wayewar litinin masu zanga-zangar sun shirye gudanar da kakkarfan yajin aikin da su ke fatan ya girgiza gwamnati a safiyar jiya Litinin, amma kuma harin ya kassara yawan jama’ar da suka yi fatan su fito don gudanar da boren.

Kawo yanzu dai bukatar masu zanga-zangar ta ganin gwamnati ta saurare su tare da mayarda hankalinta kan bukatunsa ya ci tura inda tun bayan fara gangamin a ranar 17 ga watan Oktoba ake ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin hadakar gwamnatin kasar ta Lebanon.

Shugabannin masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da gangami har zuwa lokacin da bukatarsu za ta biya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.