Isa ga babban shafi
China

Bayanan sirri sun bankado yadda China ke azabtar da musulmin Uighur

Wasu bayanan sirrin gwamnatin China sun bankado yadda mahukuntan kasar ke tsananta matakan tsaro baya ninka makullan kulle sansanin yankin Xianjing a wani mataki na hana mutanen da ke ciki galibimusulmi 'yan kabilar Uighur tserewa duk da azabtarwar da suke fuskanta.China wadda ke ikirarin cewa tana amfani da sansanonin ne na yankin Xianjing wajen koyar da karatu da kuma sana'a ga al'ummar Uighur anjima ana jita-jitar cewa ta na amfani da damar ne wajen azabtar da musulmi baya ga hana su ibada.

Sansanin Azabtar da musulmi 'yan kabilar Uighur.
Sansanin Azabtar da musulmi 'yan kabilar Uighur. REUTERS/Thomas Peter/File Photo
Talla

Bayanan sirrin wanda kungiyar 'yan jaridu da ke bincike kwa-kwaf ta bankado shi a jiya Litinin ta bayyana cewa gwamnatin China ta gindaya tsauraran matakan tsaro ta yadda ake sanya idanu kan mu'amala da zirga-zirgar musulman 'yan kabilar Uighur da ke tsare a sansanin.

Cikin matakan tsaron da China ke dauka a sansanonin rahoton ya nuna cewa hatta makewayi musulman da Uighur basu da izinin zuwa face da rakiyar jami'an tsaro, matakin da ke nuna cewa basu da damar ibada ko kuma ganawa da junansu.

Bankado asirin na gwamnatin China dai na zuwa ne makwanni bayan jaridar New York Times ta wallafa wani labarin da ke cewa shugaban China Xi Jinping ya umarci jami’ansa da kada su nuna tausayi ga ‘yan aware da masu tsautsauran ra’ayi, a wani jawabi da ya yi a shekarar 2014, biyo bayan harin da ake zargin mayakan Uighur da kaiwa wata tashar jirgin kasa.

Kafin yanzu dai China ta musanta rahotanni daban-daban da ke nuna yadda ta ke azabtar da musulmi 'yan kabilar Uighur a sansanonin da ta ke tsare da zu a yankin na Xianjing, maimakon haka sai ta fake da cewa ta bude sansanin ne da nufin koyar da sana'o'i da kuma yaren Madarin don rage tsattsauran ra'ayi ga musulmin.

A bangare guda akwai zarge-zarge da ke nuna yadda gwamnatin China ke raba 'ya'yan Musulman da iyayensu tare da hanasu aiwatar da addininsu a wani yunkuri na shafe kabilar ta Uighur da kuma addinin daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.