Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Mayakan Kurdawa na ci gaba da kauracewa arewacin Syria

Mayakan Kurdawan YPG na ci gaba da ficewa daga arewacin Syria, yankin da Turkiya ke shirin maida shin a tsaro ko tudun mun tsira.

Wasu jerin gwanon motoci dauke da fararen hula, yayin kauracewa birnin Ras al-Ain dake arewacin Syria kan iyaka da Turkiya, inda suka doshi birnin Tal Tamr dake yammacin kasar ta Syria. 19/10/2019.
Wasu jerin gwanon motoci dauke da fararen hula, yayin kauracewa birnin Ras al-Ain dake arewacin Syria kan iyaka da Turkiya, inda suka doshi birnin Tal Tamr dake yammacin kasar ta Syria. 19/10/2019. Delil SOULEIMAN / AFP
Talla

Ficewar mayakan na Kurdawa na zuwa ne, yayinda yarjejeniyar tsagaita farmakin da Turkiya ta kaddamar akansu ke shirin karewa a daren gobe talata bayan soma aiki a ranar Alhamis.

Rundunar sojin Turkiya, tace zuwa yanzu motoci 125 ne dauke da mayakan Kurdawan na YPG suka yi kaura daga yankin arewacin Syria, zuwa birnin Hasakeh dake arewa maso gabashin kasar.

A makon jiya shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan, ya ce kasarza ta kafa sansanonin dakarunta 12, domin sai ido kan yankin tsaron ko na tudun mun tsira da take shirin kafawa a arewacin kasar ta Syria.

A matakin farko dai fadin yankin tsaron da Turkiya ke son kafawa zai kai kilomita 120, a tsakanin biranen Tal Abyad da Ras al-Ain, daga bisani kuma a kara fadin yankin tudun mun tsiran zuwa kilomita 444.

Yau litinin, shugaba Erdogan yayi A-wadai da yadda kasashen yammacin Turai suka ki taimakawa Turkiya kan aniyarta ta murkushe mayakan Kurdawan, tare kuma da zarginsu da marawa ‘yan ta’adda baya, wato mayakan Kurdawan na YPG da Turkiya ta bayyana a matsayin reshen haramtacciyar jam’iyyar PKK da ta soma tada kayar baya a kasar a 1984, abinda yasa Turkiyan, Amurka da kuma kungiyar kasashen Turai bayyana ta a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.