Isa ga babban shafi
Hong Kong

'Yan majalisa sun yi wa shugabar Hong Kong ihu

Ala dole Shugabar Gwamnatin Hong Kong Carrie Lam ta dakatar da gabatar da jawabi mai kunshe da manufofin gwamnatinta a safiyar yau laraba sakamakon yadda ‘yan majalisar dokokin yankin suka yi mata ihu.

Shugabar gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam ta gaza gabatar da jawabinta kai tsaye a zauren majalisar dokokin yankin
Shugabar gwamnatin Hong Kong, Carrie Lam ta gaza gabatar da jawabinta kai tsaye a zauren majalisar dokokin yankin REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Carrie Lam, ta yi kokarin gabatar da jawabin ne don sake samun yardar jama’a da kuma ‘yan majalisar yankin, bayan share tsawon watanni ana tarzomar kin jinin gwamnatin da take jagoranta.

Sau biyu ana katse mata jawabin nata bayan ‘yan adawa a majalisar dokokin sun bige da ihun babu kakkautawa tare da bukatar ta da ta yi murabus, lamarin da ya tilasta mata gabatar da jawabin ta kafar bidiyo wanda daga bisani aka yada a shafin intanet na majalisar dokokin.

Wannan dai na nufin cewa, an gaza janye kudirn dokar tasa keyar masu laifi zuwa China a hukumance , kudirin dokar da ya haifar da zanga-zangar watanni a yankin na Hong Kong.

A cikin watan Yulin da ya gabata ne, aka dakatar da kudirin dokar, amma a wannan Larabar ne aka za ci cewa, za a janye shi a hukumance bayan ganawarta da majalisar, amma hakan ya ci tura, inda ‘yan adawa suka yi ta hawa kan tebura tare da yi wa Lami ihu.

Zanga-zangar ce dai ta tilasta wa majalisar dokokin tafiya hutun dole bayan masu boren sun far wa zauren majalisar a cikin watan Yuli.

A karon farko kenan tun shekarar 1948 da wani shugaban yankin Hong Kong ke gaza gabatar da irin wannan jawabin kai tsaye da aka saba bisa al’ada a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.