Isa ga babban shafi
Saudiya-Iran

Saudiya ta nemi shiga tsakani game da hari kan sashen makamashinta

Kasar Saudi Arabia ta bukaci kasashen duniya su shiga tsakani wajen daukar matakai game da hare-haren da ake kaiwa manyan tankokin kasashen yankin Gulf da kuma sashen makamashi, ciki har da hari kan tankokin ta biyu cikin makon nan.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Khalid al-Falih, ministan makamashi a Saudiyan, ya ce hare-haren da ake ka iwa kan makamashin kasashen yankin na Gulf babbar barazana ce da ke bukatar shigowar kasashen duniya.

Ka zalika, ministan yayin jawabinsa a taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da ke gudana a Japan bayan harin kan tankokin Saudiya ranar Alhamis, ya dora alhakin harin kan Iran da ke matsayin babbar abokiyar dabin Saudiyan.

Shima dai shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ce ke da alhakin kai harin, don kuwa a cewar sa makaman da aka yi amfani da su samfurinta ne,ko da dai tuni Tehran ta musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.